Karshen mairo
Bawani abubuwa ya iya siyaba kasantuwar komai yina ganinsa kamar old modern ɗinsune,Wanda suka zama unfinished shine aka tarkato Bawani abubuwa ya iya siyaba kasantuwar komai yina ganinsa kamar old modern ɗinsune,Wanda suka zama unfinished shine aka tarkato aka kawo Nigeria su yaya, duk da a ganin mutane irin wannan wajen shopping ɗin sai wanda yikeji da kansa yike iya shiga saboda tsadar kayansu kasantuwar sune kaɗai akaf Nigeria suke safaran irin nau’inan kayayyakin larabawa dana turawa maras algusu ,fresh and ordered one.
A gurin biyan kuɗin yaje ya tadda cashier ɗin su don yabiya kuɗinsa, wacce ta kasance macece bayarbiya ,wani irin shigan tsokano magana tayi,kai yasha attachment har ɗuwawu sai ido zarozaro da gashin ido fuska ɗau yasha fenti.
Saurin kauda kai yayi a fuskar ta don gaskiya tanada muni amma kuma bazai iya tafiya yabar ladansa ba danfa kayan jikin ta ba ƙarya ,ya kwaso mata mmartaban jikinta ya bayyana su.
kowata ballagazar arniyan bazata iya shigan da zai ɗara hakanba, a dai wajen maras mafaɗi. Lura da yanda ya zamo golo a gaban ta da yayi yasa ta soma karkaɗa na shanun ta tana daɗa balance akan kujera.
Bubbuga Automatic calculator ɗin wajen tayi mai haɗe da computer .siyyyyy saiga invoice na siyayyansa ya fito ,saida ta sa hannu ta kautar da gashinda ya zubo a gefen fuskanta
“Oga here is the receipt now you can go”(oga ga resit ɗin yanzu zaka iya tafiya)
Rasa ma mai zaiyi yayi kawai sai ya ciro bandir ɗin kuɗi ya miƙa mata .
Zaro ido tayi tana kallon sa
“Sir me zanyi dashi”
“Ladair ittakhiz haza “(ba matsala ki riƙe wannan) tunafa ashe larabci yayi mata yayi ,sai yace “oh sorry take it no problem”(oh yi haƙuri ki amsa ba matsala ai)
Wawwaigawa tashigayi saida taga bamai ganinsu tayi wuf ta warce kuɗin ta jefa a jaka ,kafin ta gyara zamanta, tana murmushi
“Thank you sir,when we will meet and at where? Coz am pretty sure you need something from me “(Nagode yallaɓai aina zamu haɗu ,kuma yaushe? Saboda nasan akwai abinda kake so a wajena)
Zaro complimentary card ɗinsa yayi mai ɗauke da adreshinsa da numbern waya
ya aje mata a gaban tebur yayi tafiyarsa .
Sura tayi ta tsaya tana karantawa,kawai saitayi zubut ta miƙe tana rawa tana waƙa
“Eeeh cinike ooohohh olu dumare …kai i thank you God…heeeee” haka tayi ta hauka da sumbatu.
Har saida taga wasu costomers na zuwa kafin ta natsu
Comments
Post a Comment